Gwamnan Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum tare da jami’an ma’aikatar kula da ayyukan jin kai ta tarayya sun isa Kamaru domin dawo da ‘yan Najeriya 9,800‘ yan asalin Borno.
Yan Najeriya 9,800 sun kasance rukunin farko na’ daga cikin mutane 46,000 da ke neman mafaka a sansanin Minawao kuma waɗanda suka bukaci komawa a gidajen su da Gwamnatin Borno ta gina a garuruwan Bama da Banki.
A watan Satumbar 2019, Zulum a yayin tafiyarsa zuwa sansanin, ya yi wa ‘yan kasa alkawarin dawo da su gida domin cigaba da harkokin su kamar yanda suka.