fbpx
Tuesday, September 29
Shadow

Gwamna Zulum ya kai ziyarar ba zata kananan hukumomin Borno saidai ya iske shuwagabannin kananan hukumomin basa bakin aiki

Gwamnan jihar Borno Babagana Umara Zulum ya bayyana cewa ya kai ziyarar ba zata kananan hukumomin jihar 6 inda ya iske shuwagabannin kananan hukomomin basa bakin aiki.

 

Sanarwar ta bayyana cewa hakan ya farune duk da cewa sati 2 da suka gabata gwamnan ya bada umarnin a dawo a ci gaba da aiki.

Yace dama tun kamun zuwan Coronavirus/COVID-19 ya samu rahotannin cewa shuwagabannin kananan hukumomin Askira-Uba, Bama, Gwoza, Damboa da Chibok basa zuwa wajan aiki, a Maiduguri suke zaune sai idan za’a kaiwa kananan hukumomin kasonsu ko kuma zai kai ziyarane suke zuwa.

 

Yace yayi gargadi akan hakan inda ya bukaci shuwagabannin kananan hukumomin su rika kasancewa a kananan hukumominsu dan mutane su san ana yi dasu amma ga dukkan alamu basu ji gargadin nashi ba, yace dan haka zai dauki mataki dan ba zai bari haka ta ci gaba da faruwa ba.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=hdlabarai.aplibwxLeave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *