fbpx
Wednesday, October 21
Shadow

Gwamna Zulum ya nemi jama’ar Borno su tashi da Azumi gobe dan addu’ar kawo karshen Boko Haram

Gwamnan Borno Babagana Umara Zulum ya umarci al’ummar jihar da su ɗauki azumi a gobe Litinin domin yin addu’o’in kawo ƙarshen rikicin Boko Haram.

Gwamnan ya ayyana Litinin a matsayin rana ta biyu ta azumi a faɗin jihar ne ranar Asabar yayin da yake jawabi a wurin wani taron masu ruwa da tsaki da ya jagoranta a Maiduguri, babban birnin jihar.

Zulum ya ce ɗaya daga cikin hanyoyin da mutane za su taimaka a yaƙi da Boko Haram ita ce, kar su shiga ƙungiyoyin ‘yan bindiga sannan su riƙa taimaka wa sojoji da bayanai da kuma yin addu’o’i.

“Bisa wannan yunƙruin ne na kirawo taro da Mai Alfarma Shehun Borno da Babban Limami da limaman masallatan Juma’a da shugabannin Kiristoci muka tattauna,” in ji shi.

“Biyo bayan wannan tattaunawa, na ayyana Litinin, 19 ga watan Oktoba a matsayin ranar azumi a karo na biyu da kuma addu’o’i a Jihar Borno.

“Ina roƙon mu fara wannan azumi da shauƙi da jajircewa kamar na ranar 24 ga watan Fabarairun 2020.”

Gwamnan ya jaddada cewa babu hutun aiki a ranar Litinin ɗin sannan kuma ya ce babu wani taron jama’a. “Abin da ake buƙata kawai shi ne tsarkake zuciya tare da yin addu’o’i daga gidajemmu,” in ji Zulum.

Yaƙin Boko Haram ya jawo asarar ran mutum fiye da 36,000 tun daga shekarar 2009, a cewar Majalisar Ɗinkin Duniya, wasu fiye da miliyan uku suka rasa matsugunansu – mafi yawa a Jihar Borno.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=hdlabarai.aplibwxLeave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *