fbpx
Tuesday, July 5
Shadow

Gwamna Zulum ya roki hukumar NEMA ta taimakawa ‘yan gudun hijira 800,000 da ke bukatar abinci a Borno

Gwamna Babagana Zulum na Borno ya nemi agajin gaggawa daga Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Kasa (NEMA) kan mawuyacin halin da kimanin mutane 800,000 da suka rasa muhallinsu ke cikin bukatar abinci a yankunan da ke fama da tashin hankali a jihar.

Bayanin na cikin wata sanarwa ce ta Malam Isa Gusau, mai ba gwamna shawara na musamman kan harkokin sadarwa da dabaru, a ranar Juma’a a Maiduguri.
Gusau ya bayyana cewa gwamnan ya yi rokon ne a wata wasika da ya gabatar yayin wata ziyara da ya kai hedikwatar NEMA a Abuja ranar Alhamis, inda ya sanar da shugaban hukumar game da mahimmancin bukatun ‘Yan Gudun Hijira (IDPs) a cikin garuruwa 11.
Hadimin gwamnan ya ce “Gwamna Zulum a cikin wata wasika, ya sanar da Darakta Janar na NEMA, AVM Muhammadu Alhaji Mohammed mai ritaya, cewa‘ yan gudun hijirar a Monguno, Bama, Damboa, Gwoza, Dikwa, Gamboru, Ngala, Damasak, Banki, Pulka da Gajiram suna bukata cikin gaggawa kayan abinci. ”
Gusau ya bayyana cewa, gwamnan ya amince da ayyukan NEMA, Hukumar Raya yankin Arewa maso Gabas da kuma kokarin da Hukumar Kwastam ta Najeriya ta yi, biyo bayan umarnin da shugaban kasa ya bayar shekaru biyu da suka gabata cewa a yi amfani da damar kwace kayan abinci don taimakon jin kai a yankunan rikici.
Ya ce “Zulum ya kuma lura da cewa dole ne a ci gaba da ayyukan abinci saboda yawancin ‘yan gudun hijirar sun dogara ne da noma a matsayin hanyar samun abinci, kuma yawancin su ba za su iya samun damar zuwa gonakin su ba saboda hare-haren masu tayar da kayar baya.”
Ya ambato babban daraktan NEMA yana tabbatar wa gwamnan Borno na ci gaba da goyon baya, kuma ya yaba da kokarin da gwamnatin Zulum ke yi na sauya jihar ta hanyar kyakkyawan shirin ci gaba.
Shugaban na NEMA ya kuma tabbatar wa Zulum da tallafin hukumar, musamman wajen aiwatar da shirin ci gaban jihar na shekaru 25 da aka bayyana kwanan nan.
Zulum ya kuma gana da Ministan Harkokin Waje, Geoffrey Onyema, game da kokarin gwamnati na dawo da dubban ‘yan asalin Borno da rikici ya raba da muhallansu, wanda a yanzu suka samu mafaka a Kamaru a cikin shekaru shida da suka gabata.
Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa akwai sama da irin wadannan ‘yan gudun hijira 60,000 a sansanin Minawawo da ke Kamaru, suna jiran a kwashe su.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Karanta wannan  Shugaban Hukumar zabe yayi tsokaci akan rahotannin dake bayyana cewa sun bude wuraren yin rigistar katin zabe a kasashen waje

Leave a Reply

Your email address will not be published.