fbpx
Tuesday, May 17
Shadow

Gwamna Zulum Ya Yi Wa Sojojin Nijeriya Kaca-kaca Bayan Harin Boko Haram A Garin Auno

Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum ya bayyana bacin ransa bisa yadda Sojoji suke aiki a jahar Borno, har ma ya dakawa babban kwamandan yaki da Boko Haram tsawa saboda yadda suke cutar da jama’a a jihar.

Jaridar The Cables ta ruwaito gwamnan ya nuna bacin ransa ne a jiya Litinin, yayin ziyarar gani da ido da ya kai garin Auno na jihar Borno inda mayakan Boko Haram suka kai farmaki suka kashe mutane fiye da 30.
A yayin ziyarar, Zulum ya zargi Sojoji da barin mutane a hannun Boko Haram, inda yace Sojojin daya kamata su samar da tsaro a Auno, amma sai ka ga sun yi tafiyarsu da an ce karfe 5 na yamma ta yi.
Boko Haram sun kai harin ne bayan Sojoji sun rufe hanyar shiga garin Maiduguri daga karfe 5 na yamma kamar yadda dokar ta baci ta tanada, hakan yasa suka datse jama’a da dama a waje, wadannan jama’an ne Boko Haram ta kai ma farmaki ta karkashesu, sa’annan ta kona motocinsu.
Da yake yi ma kwamandan Operation Lafiya Dole bayani, Sunday Igbinomwanhia a inda lamarin ya auku a ranar Litinin, Zulum yace: “Dole ne mu fito fili mu fada muku gaskiya, tunda na zama gwamna Boko Haram sun kai hari Auno sau 6, kuma Sojoji sun fice daga garin Auno.
“Ba wai na raina aikin Sojoji bane, amma mun sha muku magana a kan cewa ya kamata ku kafa sansani a Auno, amma sai ku shiga garin, da zarar an ce 5 ta yi sai ku rufe kofa ta kulle mutane a waje, ku kuma ku koma Maiduguri, wannan bai kamata ba.” Gwamnan ya fada yana daga murya cikin fushi, yayin da jama’a ke masa tafi.


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Karanta wannan  Kundumewa Deborah: Kungiya ta nemi a kamo limamin BUK bisa zargin halasta jini+@n Bishop Kukah


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.