A yayin da ‘yan Najeriya musamman lauyoyi suka yi chaa akan gwamnan babban bankin Najeriya, Godwin Emefiele game da maganar fitowa takarar shugaban kasarsa, gwamnan ya garzaya kotu.
Lauyoyin na cewa, ci gaba da kasancewar Emefiele a matsayin gwamnan babban bankin Najeriya abune me matukar hadari tunda ya shiga siyasa.
Saidai lauyan gwamnan ya tafi kotu inda yake neman a mai bayani me doka tace kan wannan lamari.
Emefiele dai bai bayyana cewa ya fito takarar shugaban kasa ba amma yace yana jiran taimakon Allah akan lamarin.
Duk da kungiyar manoma shinkafa sun sai masa fom din takarar, yace idan zai fito, shine da kansa zai saiwa kansa Fom din.