Gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello ya nuna rashin yarda da Cibiyar Kula da Cututtuka ta Najeriya NCDC game da musabbabin mutuwar Babban Alkalin jihar, Mai shari’a Nasir Ajana.
Mai shari’a Ajana ya mutu a ranar Lahadin da ta gabata a cibiyar kebewa dake Gwagwalada COVID-19.
Gwamnan, wanda yake magana a yayin addu’o’in ranar uku ga mamacin a ranar Talata, ya ce marigayi Babban Alkali ya mutune amma ba cutar Korona ce ta kashe shiba inda ya bukaci jama’a da kada su danganta mutuwarsa da komai.
Gwamnan ya bayyana marigayi CJ a matsayin mutumin kwarai da kuma mai son zaman lafiya.
Daman ba tun yanzu ba gwamanan jihar ke hawa dokin naki kan yadda cibiyar yaki da cututtuka ta kasa ke tafiyar da lamuranta akan rahotanin cutar Coronavirus a kasar, inda ake jiyo aman gwamanan na suka tare da musanta rade rade bullar cutar a jihar tasa.