fbpx
Saturday, August 20
Shadow

Gwamnan Benue na so Buhari ya ayyana Miyetti Allah a matsayin kungiyar ‘yan ta’adda

Gwamnan jihar Binuwai a Najeriya Samuel Ortom, ya yi kira ga shugaban ƙasar ya kuma ayyana wasu ƙungiyoyin Fulani makiyaya kamar Miyetti Allah Kautal Hore da Kungiyar Mi Yetti Allah (wato MACBAN), da kuma Fulani Nationality Movement (wato FUNAM) a matsayin ‘yan ta’adda su ma.

A cewar Gwamna Ortom ayyana ‘yan fashin daji a matsayin ‘yan ta’adda kaɗai da gwamnatin Najeriya ta yi bai isa ba.

Ya dai zargi ƙungiyoyin Fulanin da lasar takobi da kuma ci gaba da haddasa gagarumin yamutsi a jihar Binuwai da ma sauran yankunan ƙasar saboda dokokin hana kiwon sake.

Karanta wannan  Da Duminsa: NBC ta kwace lasisin gidajen talabijin na Silverbird, AIT, Gidan radiyon Raypower, Rhythm FM da sauransu

Ɗaya daga cikin kungiyoyin da gwamnan ya ambata dai ta yi watsi da wannan kira, wanda suka bayyana da cewa, wani bi ta da kulli ne kawai.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.