fbpx
Monday, March 1
Shadow

Gwamnan Ekiti ya bukaci mazauna garin su dauki ‘yan sanda a matsayin abokan su

Gwamnan jihar Ekiti, Kayode Fayemi, ya bukaci mazauna jihar da su ajiye duk wata rashin fahimta akan abubuwan da suka faru a baya sakamakon zanga-zangar adawa da runduar SARS, A cewarsa ya dace Al’umma su Dauki jami’an ‘yan sanda A matsayin Abokanan su.

Gwamnan ya bayyana cewa Zanga-zangar data faru a baya ta haifar da abubuwa marasa dadin ji Dan haka yayi kira da Al’ummar jihar da su cigaba da Nuna goyan bayan su ga Jami’an tsaro domin samun hadin kai a kasa baki daya.

Gwamnan ya fadi hakan ne a garin Ikere-Ekiti A ranar Asabar yayin da yake kaddamar da sabuwar hedikwatar ‘yan sanda a jihar.

 

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *