fbpx
Thursday, August 18
Shadow

Gwamnan jihar Ekiti ya Tsige Shugaban kwamitin wasanni na jihar

Gwamnatin jihar Ekiti ta dakatar da nadin Mista Isaac Ayodele a matsayin Shugaban kwamitin wasanni na jihar.

Wannan na kunshe ne, a wata wasika da kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) ya samu a ranar Asabar a Ado-Ekiti.

Wasikar, mai dauke da kwanan watan 19 ga Nuwamba, tare da sa hannun Sakataren Gwamnatin jihar Ekiti (SSG), Mista Biodun Oyebanji, wanda kuma aka aike ta izuwa  ga Ayodele a ranar 20 ga Nuwamba.

Wasikar wadda ke kunshe da batun sallama tare da bukatar Shugaban kwamin da ya ajiye aikin sa nan take.

Sai dai har zuwa yanzu babu wani karin haske kan dalilin sallamar.

 

 

 

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.