fbpx
Tuesday, July 5
Shadow

Gwamnan Jihar Enugu Ifeanyi Ugwuanyi ya bayar da umarnin sake gina wasu masallatai biyu da aka lalata a jihar

Gwamnan Jihar Enugu Ifeanyi Ugwuanyi ya bayar da umarnin sake gina wasu masallatai biyu da aka lalata a jihar yayin hatsaniyar da ta faru a satin da ya wuce.

Masu zanga-zangar sun lalata masallatan ne a yankin Nsukka na jihar dake a kudu maso gabashin kasar.

Shugaban karamar hukumar Nsukka Mista Cosmas Ugwueze ne ya bayyana hakan yayin ziyarar da ya kai masallatan da abin ya shafa a madadin gwamnan jihar.

 

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.