fbpx
Saturday, May 28
Shadow

Gwamnan jihar Kaduna ya zama abin koyi ga sauran gwamnonin kasarnan akan gyaran Ilimi

Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasiru El-Rufai ya zama abin koyi ga sauran gwamnonin jihohin kasarnan musamman Arewa, akan yiwan malaman firaimare jarabawa da kuma tantance wadanda suka cancanta sannan a sallami wadanda basu cancantaba.

Kwanannan ne gwamnan ya shiryawa malaman firaimare na jihar jarabawar ‘ yan aji hudu amma sakamakon jarabawar ya nuna cewa guda dubu ashirin da biyu sun fadi kuma gwamnan zai sallamesu aiki ya dauki wasu sabbin malam su dubu ashirin da biyar.

Wannan batu ya dauki hankulan mutane sosai inda wasu dake tausayawa malaman da za’a kora suka bayyana cewa bai kamata a koresuba, kamata yayi a basu horaswa ta musamman ko kuma a mayar dasu wata ma’aikatar inda ba zasuyi koyarwa ba, tunda ba dadi mutum da iyali a kulle mishi hanyar samu.

Wasu kuma sun bayyana cewa tunda malaman basu cancantaba kawai a sallamesu, abinda ya kamata a duba shine yaran da ake koyarwa karsu samu gurguwar ginshikin karatu.

Karanta wannan  Tsohon Hoton Farfesa Osinbajo da iyayensa lokacin da ya gama makaranta

To yanzu dai wannan batu ya kusan zuwa karshe domin rahotanni sun bayyana cewa gwamnan na jihar Kaduna yana kokarin duba ma’aikatar da zai saka malaman da suka fadi jarabawar su cigaba da aiki dan kar a sallamesu.

Yanzu haka dai gwamnatin jihar kogi ta aikawa gwamnatin jihar ta Kaduna tawagar wakilai dan a nuna musu yanda aka gudanar da irin wannan tsari na tantance malamai dan suma suyi, kuma an dankamusu takardar data kunshi yanda akayi wannan tsari.

Ko a jiya dai saida rahotanni suka bayyana cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi na’am da wannan tsari da gwamnan jihar Kaduna ya dauka na gyaran ilimi a jihar ta Kaduna.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.