fbpx
Friday, January 15
Shadow

Gwamnan jihar Kano ya bada umarnin gudanar da gwajin miyagun kwayoyi ga ‘yan takarar kananan hukumomin Jihar

Gwamna Abdullahi Ganduje ya umarci dukkan wadanda suka fito takara a zabukan kananan hukumomi da ke tafe wanda aka shirya gudanarwa a ranar 16 ga watan Janairun sabuwar shekara, da su tabbata an yi musu gwajin muggan kwayoyi.

Kwamishinan yada labarai na jihar, Muhammad Garba ne ya bayyana hakan a ranar Alhamis yayin da yake yi wa manema labarai bayani kan sakamakon taron majalisar zartarwa na jihar da aka gudanar a gidan gwamnatin Kano.

A cewar Mista Garba, Gwamnatin jihar ta yanke shawarar yin hakan ne domin tsabtace jihar Kano daga shan muggan kwayoyi.

Ya kuma sake jaddada aniyar gwamnatin jihar karkashin jagorancin Gwamna Abdullahi Ganduje na magance shan miyagun kwayoyi tsakanin shugabannin siyasa a fadin jihar.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *