fbpx
Saturday, September 19
Shadow

Gwamnan jihar Kebbi ya sha Al’washin tai makawa Monoman da Ambaliyar Ruwa ta ci Gonakin su

Gwamnan Jihar Kebbi, Abubakar Atiku Bagudu, ya jajantawa manoma da ambaliyar ruwa ta lalata gonakin su, tare da basu tabbacin cewa  gwamnati zata samar da ingantattun iri da sauran kayan aikin gona da ake bukata don ba su damar komawa gonakinsu da zarar ruwan ambaliyar ya janye.

Gwamnan ya kuma yi alkawarin shiga tsakani wajen fadada rancen manoman.

Gwamna Bagudu ya bayar da wannan tabbacin ne yayin ziyarar da ya kai wa wasu al’ummomin da ambaliyar ta shafa a kananan hukumomin Dandi da Koko Besse.

 

Da yake jawabi tun farko, Shugaban Kauyen Tungar Rahi, Alhaji Rabiu Hakimi, wanda ya yi magana a madadin manoman, ya roki gwamnan da ya shiga tsakani a madadinsu domin jinkirta biyan bashin manoma har zuwa 2021.

Da yake amsawa, Gwamna Bagudu ya ba su tabbacin cewa zai shiga tsakani dangane da rokonsu na tsawaita biyan bashin.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=hdlabarai.aplibwxLeave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *