Gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello ya bayyana matukar kaduwa game da mutuwar tsohon Ministan Shari’a kuma Babban Lauyan Tarayya Abdullahi Ibrahim (SAN), yana mai bayyana rasuwarsa a matsayin rashi ne ga kasar da jihar baki daya.
Mirgayin Dan kabilar Igala ne wanda ya fito daga yankin gabashin jihar Kogi, ya rasu ne a ranar Lahadi 24 ga watan Janairun 2021, kuma shine SAN na farko daga Arewacin Nijeriya haka kuma ya yi aiki a matsayin Babban Lauyan Tarayya A tsakanin shekarar Alif 1997 da kuma Alif 1999.
Sakon ta’aziyyar ya fito ne daga bakin, Babban Sakataren yada labaran na gwamna Bello, Onogwu Muhammed wanda ya fitar, inda ya bayyana marigayin Abdullahi a matsayin kwararren masanin shari’a kuma mai aiki da kwarewa.