Wani Mummunan hadarin mota da ya afku a jihar kogi a kauyan Akpata da ke karamar hukumar Lokoja na jihar yayi sanadin mutuwar mutane 14 tare da jikkata wasu da dama.
An rawaito cewa, Hadarin ya faru ne lokacin da wata mota dauke da fasinja tai taho mugama da wata motar daukar kaya dauke da siminti lamarin da yayi sanadin salwantar rayukan mutum 14.
A wani sakon jaje da Gwamnan Jihar Yahaya Bello ya aikewa wadanda lamarin ya rutsa dasu ta hannun kwamishinan jihar Kingsley Fanwo ya nuna matukar damuwarsa tare da yin kira da hukumar Kiyaye hadura ta jihar kan ta tsaurara tsaro da sa’ido a kan hanyoyin jihar.