Gwamnan jihar Kogi Yahaya Bello ya bayyana cewa kwanan nan wasu abokanan sa gwamnonin PDP zasu kama jam’iyyar APC.
Da yake zantawa da tashar talabijin ta Channel Gwamna Yahaya Bello ya bayyana cewa nan gaba kadan wasu abokanan sa gwamnonin jam’iyyar Adawa ta PDP su akalla 10 zasu dawo jam’iyyarsa mai mulkin Najeriya wato APC.
Da yake mayar da amsar tambayar cewa ko shin jama’iyyar APC zata durkushe bayan Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bar kujerar mulki a shekarar 2023, sai ya ce kokadan illama jam’iyyar APC zata kara karfine.
Haka zalika Gwamnan ya bayyana takaicin sa na ficewar gwamnan jihar Edo Obadeki daga jam’iyyar APC inda ya sha al’washin cewa lalle nan gaba zaiyi komayya cikin jam’iyyar sa ta asali APC.