fbpx
Wednesday, August 10
Shadow

Gwamnan jihar Lagas, Sanwo-Olu zai dakatar da biyan fansho ga Tinubu da sauran tsaffin Gwamnonin jihar

Gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu, ya ce zai soke wata dokar Ofishin Jihar (wadda aka kafa ta don Fansho a 2007), wacce ke baiwa tsoffin gwamnonin jihar dama amsar fanso da wasu kudade bayan sauka daga mulki.
Gwamnan ya fadi haka ne lokacin da yake gabatar da kasafin kudi na 2021 a gaban majalisar dokokin jihar Legas.
Doka ta tanadi biyan fansho da sauran hakkoki ga tsoffin Gwamnoni da mataimakan su a jihar.
Kwamishinan yada labarai na jihar Legas, Gbenga Omotoso ne ya nakalto shi:
“Bisa la’akari da rage kudin da ake kashewa wajen gudanar da mulki da kuma nuna rashin son kai a aikin gwamnati, za mu aika da daftarin kudirin doka ga Majalisar nan ba da dadewa ba don soke wasu kudirorin Ofishin Jihar wadanda akayi don Dokar Fanshon 2007, wanda ya tanadi biyan fansho da sauran kudade ga tsoffin gwamnoni da mataimakan su.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Karanta wannan  Sanata Shehu Sani ya cewa gwamnonin da suka baiwa Buhari shawara ya sallami ma'aikatan da wuce shekara hamsi su fara kansu

Leave a Reply

Your email address will not be published.