fbpx
Wednesday, August 10
Shadow

Gwamnan jihar Rivers, Nyesom Wike ya shilla kasar Turkiyya don shakatawa

Gwamnan jihar Rivers wanda ya fadi zaben fidda gwani na shugaban kasa a jam’iyyar PDP, Nyesom ya shilla kasar Tuekiyya don holewa.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a shafinsa na Twitter, kuma ya kai ziyarci kasar ne tare da abokinsa tsohon gwamnan jihar Abia, Okezie Ikpaezu.

Gwamna Wike ya karbi bakuncin manyan ‘yan siyasar Najeriya kafin ya tafi kasar a cikin makon daya gabata.

Inda dan takarar shugaban kasa na NNPP Rabi’u Kwankwaso dana Labour Party Peter Obi suka kai masa ziyara a gidansa na Patakwal, kuma gwamna Umahi ma ya kai masa ziyara.

Leave a Reply

Your email address will not be published.