fbpx
Wednesday, August 10
Shadow

Gwamnan Kaduna ya bukaci hadimansa su bayar da tallafin Dubu Dari 5 kowannensu

A sanarwar da ya fitar ta tsawaita zaman gida dole dan dakile yaduwar cutar Coronavirus/COVID-19 a Kaduna, Gwamna Malam Nasiru Ahmad El-Rufai ya bukaci masu rike da mukaman siyasa, hadimansa a jihar da kowannensu ya bayar da tallafin Naira Dubu Dari 5.

 

Gwamnan ya kuma kara da cewa daga yanzu za’a rika cirewa masu rike da mukaman siyasar kaso 50 cikin 100 na albashinsu har sai maganar killacewar ta wuce.

 

Sanarwar wadda ta fito daga hannun me baiwa gwamnan shawara ta fannin sadarwa,Muyiwa Adekeye ta kara da cewa su kuma ma’aikata masu daukar Albashin sama sa Naira Dubu 67 za’a rika cire musu kaso 25 cikin 100 na Albashinsu.

Karanta wannan  Hotuna: Kungiyar kiwon lafiya ta kaiwa shugaba Buhari ziyara a fadarsa

 

Karin abinda sanarwar ta kunsa shine samar da kotun tafi da gidanka dan yankewa wanda suka karya dokar jihar hukunci nan take.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.