by Abubakar Saddiq
Gwamnan kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya amince da a ringa bude mayankan Abbatuwa a ranakun Litinin da Alhamis da aka sassauta dokar a jihar.
Ganduje ya bayyana hakan ne a lokacin da yake kaddamar da rabon tallafin kyallen rufe hanci ga al’umma.
A cewar rahoton an bude mayankan Abbatuwa ne a sakamakon rashin tsaftar da ake samu a unguwanni a yayin yankan dabbobi.