Monday, December 9
Shadow

Gwamnan Katsina ya ƙaddamar da ƙarin dakarun tsaro na jihar

Gwamnan Katsina ya ƙaddamar da ƙarin dakarun tsaro na jihar.

Gwamnatin jihar Katsina da ke arewacin Najeriya ta ƙaddamar da sabbin rukunin jami’an tsaro na da ake kira KTS C-Watch.

Dakarun tsaron unguwannin 550 su ne kashi na biyu da Gwamna Dikko Umaru Radda ya ƙaddamar a yau Juma’a da zimmar yaƙi da ‘yanfashin daji masu sacewa da kashe mutane haka kawai.

“Mun ɗauki mutum 6,652 domin daƙile matsalar tsaro. Sannan mun nemi masu gari, da limamai, da ladanai, tare da ba su albashi a matsayin wani ɓangare na shirin samar da tsaro a unguwanni,” a cewar gwamnan.

Karanta Wannan  Obasanjo Ya Ziyarci Uwargidan Shugaban Kasa Bayan 'Yan Kwanaki An Hange Shi Sanye Da Hula Kalar Tambarin Tinubu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *