Gwamnan jihar Kogi, Yahya Bello ya bayyana cewa, akwai maciya amana a tare dashi kuma zai yi maganinsu.
Gwamnan ya bayyana hakane a yayin ganawa da wasu masu ruwa da tsaki a jam’iyyar APC ta jihar Kogin.
Yace akwai wanda ya musu sha tara ta arziki amma suna munafurtarsa. Yace sai ya tabbatar sun dandana kudarsu.
Rahoton dailypost dai yace gwamna Yahya Bello ya samu tirjiya daga jam’iyyarsa saboda zabar Ododo a matsayin wanda zai gajeshi.