Gwamnan jihar Kwara, Abdulrahman Abdulrazaq ya bayyana cewa ya bayar da Albashinsa na wata 10 gaba daya ga jihar dan a yaki cutar Coronavirus/COVID-19.
Gwamnan ya bayyana hakane a wata sanarwa daya fitar ta hannun sakataren watsa labaransa, Rauf Ajakaye inda ya kuma bayar da umarnin a fara rabawa al’ummar kayan Abinci gida-gida.
Gwamnan yayi kira ga jama’ar jiharsa da su ci gaba da zama a gida tare da nesa-nesa da juna dan kaucewa yaduwar cutar.
Ya bayyana cewa ya dauki wannan matakine saboda akwai bukatar sadaukarwa a wannan lokacin.
Ya kara da cewa duk da yake cutar bata shiga jiharshi ba amma zai yi dukkan mai yiyuwa dan ganin ya kare al’ummarsa.