fbpx
Wednesday, February 24
Shadow

Gwamnan Neja Abubakar Sani Bello ya sha Al’washin kara kaimi wajan tabbatar da tsaro a jiharsa

Gwamna Abubakar Sani Bello na jihar Neja ya yi Allah wadai da kakkausar murya game da sace fasinjoji 20 a kauyen Kundu da ke karamar hukumar Rafi ta jihar Neja.

Gwamna Sani Bello a cikin wata sanarwa ya bayyana lamarin a matsayin halin rashin kirki, inda ya kara da cewa gwamnati za ta kara kaimi wajen tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyi.

Gwamnan ya ci gaba da cewa gwamnatinsa ba za ta mika wuya ga masu aikata miyagun laifuffuka a jihar ba da suka hada da ‘yan fashi, masu satar mutane da barayin shanu, A cewarsa Gwamnatinsa zata ci gaba da amfani da wadatattun kayan aiki da ma’aikata don dakile matsalar.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *