Gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle ya bayyana hanya da ya da za’a iya magance matsalar tsaro.
Yayi zargin cewa, ‘yan Bindigar a hankali suna komawa jiharsa ta Zamfara.
Gwamna Bello yace ‘yan siyasa na da hannu a lamarin inda suke daukar mutane a matsayin masu bayar da bayanan sirri.
Kakakin Gwamnan, Zailani Bappa ya bayyana cewa wasu manyan mutanene ke mayar da ‘yan Bindiga jihar ta Zamfara.
Gwamnan ya bayyana cewa, shiyasa ya kira ‘yan siyasar jihar da su zo su rantse da kur’ani basa daukar nauyin ‘yan Bindiga amma wasu suka kiya.
Yace shi a ganinsa wannan itace hanya daya tilo da za a iya magance matsalar ta ‘yan Bindiga.
Gwamnan yace ya samu nasara sosai wajan yakar ‘yan Bindigar a jihar Zamfara.