fbpx
Thursday, August 11
Shadow

Gwamnati ba da gaske take ba kan yaki da matsakar tsaro>>Sanata Ali Ndume

Sanata Ali Ndume wanda shine shugaban kwamitin dake kula da bangaren tsaro ya bayyana cewa, gwamnatin tarayya ba da gaske take ba wajan yaki da matsalar tsaro.

 

Ya bayyana hakane saboda a cewarsa, har yanzu gwamnatin ta kasa zakulo masu hannu a kan ayyukam tsaron ta bayyanawa ‘yan Najeriya sunayensu.

 

Ya bayyana cewa an taba kamashi akan cewa yana da alaka da Boko Haram.  Ya caccaki jami’an tsaro kan yanda suke dorawa mutum zarfi ba tare da cikakken bincike ba.

Karanta wannan  Majalissar dinkin duniya tace harkar Crypto zata iya rusa Najeriya da sauran kasashen da suka cigaba

 

A shekarar 2011 ne aka taba kama Sanata Ali Ndume bisa zargin alaka da Boko Haram amma kotu ta wankeshi.

 

Sanata Ali Ndume yace idan dai za’a kamashi a kaishi kotu kan irin wancan zargi to ake jira da sauran wanda ake zargi?

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.