fbpx
Monday, August 15
Shadow

Gwamnati ta amince da ayi kidayar ‘yan Najeriya a watan Afrilu na 2023

Majalisar uwayen kasa ta amince da yin kidayar ‘yan Najeriya a watan Afrilu na shekarar 2023 bayan yin zaben babban zabe.

 

Shugaban hukumar Kidaya ta kasa, Nasir Isa-Kwarra ne ya bayyana haka ga manema labarai bayan zaman majalisar a fadar shugaban kasa.

 

Yace hukumar tasa zata yi kidayar ta gwaji a watan Yuni bayan kammala zabukan fidda gwani na jam’iyyun siyasa.

 

Yace bayanan da aka dasu a yanzu sun tsufa.

 

Yace kidayar jama’a da sanin yawan ‘yan kasa na da muhimmanci sosai dan ta hanyar hakanne ake sanin yanda za’a yi ayyukan ci gaba ga Al’umma.

Leave a Reply

Your email address will not be published.