Gwamnatin jihar Ondo ta bayyana cewa ta Haramta gidajen kallon kwallo a jihar.
Gwamnan jihar, Rotimi Akeredolu ne ya bayyana haka ga manema labarai a ganawar da yayi dasu a babban birnin jihar, Akure.
Gwamnan ya saka wannan dokane bayan da ya bayyana rashin jin dadinsa kan yanda ake samun mutane na karya dokar dakile yaduwar cutar Coronavirus/COVID-19 da aka sa inda suke zuwa kallon kwallo.
Yace gwamnatinsa ba zata yi kasa a gwiwa ba wajan ganin ta saka dokokin da zasu hana cutar yaduwa a jihar ba.
Gwamnan ya kuma yi kira ga guraren ibada dasu ci gaba da kiyaye ka’idojin da aka gindaya masu.