Ministan cikin gida a Najeriya, Rauf Aregbesola, ya ce taron majalisar ministoci ya amince a kafa masana’antu biyu na ƙera takalma da sutura da sarafa leda a Janguza da ke Kano da Aba a Jahar Abia karkashin yarjejeniyar hadin-gwiwar gwamnati da kamfanoni masu zaman kansu.
Ministan ya shaidawa ƴan jarida cewa kamfanonin Najeriya ne za su aiwatar da shirin da taimakon kawaancen China.
Aregbesola ya ce aikin zai samar da ayyuka 4,330 ga ƴan kasa baya ga kuɗaɗe N5.1bn na hannun jari.