fbpx
Monday, March 1
Shadow

Gwamnatin Adamawa ta hana wasu Fulani shiga jihar

A Najeriya, waɗansu Fulani kusan 150 sun shiga halin tsaka mai wuya bayan sun yi ƙaura daga Jihar Neja zuwa Adamawa amma sai gwamnati ta ƙi karɓarsu.

A halin da ake ciki dai an tilasta musu komawa inda suka fito.

Fulanin sun yi hijira ne sakamakon hare-haren `yan bindiga da kuma zargin da suke yi cewa `yan banga na takura musu.

Sun yi kaura ne tun ranar 1 ga watan Fabarairu daga rugarsu da ke gundumar Zugurma ta jihar Neja zuwa Adamawa bayan sun shafe shekaru masu yawa suna rayuwa a wurin.

Sun ce sun guje wa rikicin da ake fama da shi a yankin na hare-haren `yan bindiga da kuma baƙin-jini da karan-tsanar da ake jingina wa Fulani makiyaya saboda ƙaurin-sunan da wasu daga cikinsu suka yi wajen satar mutane.

A karshe dai sun yi gudun gara suka fada zago, kasancewar mahukunta a jihar Adamawan ba su ba su fuska ba.

Mallam Kirowa Muhammadu, shi ne jagoran ayarin Fulanin kuma ya shida wa Ibrahim Isa cewa sun shafe kusan mako biyu suna watangaririya tsakanin jihohin Neja da Adamawa da Kaduna.

BBChausa.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *