fbpx
Wednesday, August 10
Shadow

Gwamnatin Buhari ce hedikwatar ‘yan Boko Haram, cewar dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar SDP

Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar SDP, Adebayo Adewole ya bayyana cewa matsalar tsaron Najeriya a tsakanin gwamnati da hukuma take.

Ya bayyana hakan hakan ne yayin dayake ganawa da manema labarai na Chennels a ranar laraba.

Inda ya bayyana masu cewa gwamnatin Najeriya da ‘yan ta’addan Boko Haram a hedikwata daya suke saboda haka matsalar tsaro ba za a magance ta nan kusa ba.

A karshe yace gwamnatin Najeriya kasuwanci take yi da matsalar tsaro sai yasa taki magance su, kuma yakar manyan dake marawa ‘yan ta’addan baya tafi yakar ‘yan ta’addan wahala sosai.

Leave a Reply

Your email address will not be published.