fbpx
Tuesday, July 5
Shadow

Gwamnatin Buhari ce mafi muni a tarihin Najeriya>>Bishop Oyedepo

Bishop David Oyedepo, Shugaban Cocin Living Faith Worldwide ya caccaki gwamnatin shugaban kasa,Muhammadu Buhari inda ya bayyana ta a matsayin mafi muni a tarihin Najeriya wadda kuma ta zamarwa kasar kamar wata Annoba.

 

Oyedepo ya bayyana hakane a lokacin da yake gabatar da kasida a cocin nashi dake jihar Ogun Ranar Lahadin data gabata.

 

Ya fara da caccakar kudirin dokar kalaman batanci da Sanata Sabi Abdullahi ya gabatarwa majalisar dattijai inda yace shin wai da wanda yace zai kashe ka da wanda ya kashe ka wanene ya aikata laifi?

 

Bishop Oyedepo ya bayyana cewa, kudirin dokar shirme da shahanci kawai.

Karanta wannan  Babu dan arewar da zai zabi Peter Obi, cewar Kwankwaso

 

Ya kara da cewa maimakon a mayar da hankali akan masu kashe mutane sai masu fadar gaskiyane akan gwamnati za’a rika hari. Ya kara da cewa idan gwamnatinka bata da kyau babu abinda zai hanani in fada dan ni asalin dan Najeriyane kuma ba sabon shigane a harkokinta ba.

 

Yace gwamnatin Buhari itace mafi muni kuma ta zama kamar wata annoba ga ‘yan kasar, ya kara da cewa kuma karshenta na nan zuwa.

 

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.