Gwamnatin tarayya ta baiwa iyalan insfeto na hukumar farar hula, Ilyasu Abraham naira miliyan 2.8 bayan daya mutu a harin da ‘yan Boko Haran suka kaiwa gidan kurkuku na Kuje.
A ranar biyar ga watan Yuli ne Abraham ya rasa rayuwarsa yayin dayake kan aikinsa na taimakawa kasarsa ta Najeriya a babban birnin tarayya.
Hukumar ta basu wannan kudin ne a jiya ranar alhamis kamar ta bayyana, inda kwamanda Ahmad Audi ya basu Cheque na naira miliyan 2.5 da kuma kudi naira 300,000.
Kuma a karshe yace zasu dauki diyarsa aiki wato Abimiku Abraham a daliban da zasu dauka aiki na gaba, domin su taimaka iyalan nashi.