fbpx
Thursday, May 26
Shadow

Gwamnatin Buhari ta raba kan ‘yan Najeriya ta hanyar addini da kabilanci – Bishop Kukah

Bishop din darikar Katolika na shiyyar Sokoto, Mathew Kukah ya zargi gwamnatin Buhari da raba kan ‘yan Najeriya ta hanyar addini da kabilanci.

Kukah wanda ya gargadi malaman addini da su guji fadawa tarkon ‘yan siyasa ta hanyar neman kudi a sakonsa na Easter, ya kuma kara da cewa gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari na cikin kwanciyar hankali yayin da kasar nan ta wargaje da rarrabuwar kawuna.

Ya kuma kara da cewa abin da kawai ke aiki a kasar nan shi ne cin hanci da rashawa, inda ce dole ne a ceto Najeriya daga fadawa cikin halin rashin tabbas.

Leave a Reply

Your email address will not be published.