Gwamnatin jihar jigawa tace tana biyan likitocin jihar dake kula da masu corona har kimanin Naira dubu 10 a kullum a matsayin alawus din su.
Gwamnan jihar Alhaji Muhammad Badaru Abbubakar ne ya tabbatar da hakan ga manema labarai a gidan gwamnatin dake dutse.
Yakara da cewa Gwamnatin jihar na kokarin shigar da kowanne Jami’in lafiya cikin tsarin inshora a sakamakon ha tsarin dake cikin aikin.
Gwamnan ya yaba da Jami’an dake aikin sannan ya kuma yaba musu bisa sadaukarwar da suke.