Kimanin otal biyar da ke yankin karamar hukumar Aba ta Arewa A Jihar Abia Jami’an dake sanya ido kan bin laduban cutar Coronavirus a jihar ne suka kulle.
Rahotanni sun bayyana cewa an garkame Otal-Otal din sabuda sakacin masu su na kin bin umarnin gwamnati data sanya kan cutar Covid-19.
Wata majiya ta bayyana cewa wadanda suka ki bin umarnin gwamnatin jihar a kan COVID-19 za a kama su kuma a gurfanar da su a kotun tafi da gidanka.
A halin yanzu, gwamnatin jihar Abia ta haramta duk wasu tarukan dare da ayyukan al’adu a jihar.
Haka zalika shugaban kwamitin dake yaki da cutar a jihar . Chris Ezem ya gargadi mamallakan otal din jihar da su kiyaye matakan kariya na cutar idan bahaka ba zasu fuskanci tara har ta kimanain dubu 100