Sunday, May 31
Shadow

Gwamnatin jihar Bauchi ta cimma matsaya da ‘yan kasuwar jihar don saukaka kayan masarufi inda Buhun shinkafa zai koma 17,500

Yan kasuwa a Bauchi sun amince za suna sayar da shinkafa akan dubu 17,500

Gwamnatin jihar Bauchi ta cimma matsaya da ‘yan kasuwar jihar kan sassauta farashin kayan masarufi bisa halin da al’umma suke ciki.
A Cikin wata sanarwa da Gwamnatin jihar Bauchi ta fitar da sa hannu  mataimakin gwamnan jihar kan yada labarai Mukhtar Gidado a cewar sa an yi zama na musamman tsakanin kwamnitin yaki da cutar Covid-19, da kuma bangarorin ‘yan kasuwar jihar inda aka cimma matsayar  sassauta farashin kayan masarufi.
Kayayya kin da aka cimma matsaya akan sa sune shinkafa wanada za’a na siyarwa akan Naira dubu 17,500.
Sai kuma sukari inda za’a na siyarwa akan 17,000.
Sai kuma gero akan Naira 12,500.
Manja Naira 9,000
Sai nama kilo daya kuma 1,200.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=hdlabarai.aplibwxLeave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *