fbpx
Thursday, August 18
Shadow

Gwamnatin jihar Kaduna ta ba da gudummawar kayan tallafi ga al’ummomin aka kaiwa hari

Gwamnatin Jihar Kaduna a ranar Talata ta ba da kayayyakin tallafi ga wadanda harin na ranar Lahadi ya shafa a kauyukan Ungwan Bido da Ruggan Danbarau da ke gundumar Aso ta karamar Hukumar Jema’a.
An kashe mutane takwas kuma hudu sun ji rauni a wasu hare-hare daban-daban da aka kai wa Ungwan Bido da Rugan Danbarau a ranar 29 ga watan Nuwamba bayan rashin fahimta tsakanin mazauna ƙauyukan biyu.
Da yake bayar da gudummawar kayayyakin a madadin gwamnatin jihar, Mista Abubakar Hassan, Sakataren zartarwa na Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar (SEMA) ya jajanta wa al’ummomin da abin ya shafa kan lamarin.
Hassan ya ce sun kawo ziyarar ce domin gudanar da aikin tantancewa kai tsaye ga al’ummomin da abin ya shafa, da nufin kawo karin kayayyakin agaji don taimaka musu sake gina gidajensu.
Ya ce rashin fahimta wani bangare ne na alakar dan Adam amma yadda suka warware su yana da muhimmanci.
Tun da farko, shugaban karamar hukumar, Mista Peter Averik, ya yaba da yadda gwamnatin jihar ta hanzarta wajen ba da taimako ga wadanda harin ya rutsa da su.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Karanta wannan  'Yan ta'addan ISWAP sun dauke manoma shida a jihar Borno

Leave a Reply

Your email address will not be published.