Saturday, April 4
Shadow

Gwamnatin jihar Kaduna ta saka dokar zaman gida Dole

Gwamnatin jihar Kaduna ta saka dokar zaman gida na Dole inda tace gaba dayan jama’ar jihar zasu zama a killace.

 

Mataimakiyar gwamnan jihar,Hajiya Hadiza Balarabe ce ta sanar da haka inda tace shawarar kwararrune dake kula da yanda lamurran cutar ke gudana a suka bayar aka dauka.

 

Tace maganar rufe makarantu ta yi aiki amma jama’a na ci gaba da taro da kuma gudanar da ayyukan ibada wanda kuma a baya gwamnatin ta fada cewa idan ba’a bi shawarar data bayar ba to zata saka dokar ta baci.

 

Gwamnatin tace to an kawo lokacin da zata saka dokar.

 

Ta kara da cewa dokar zata fara aikine da karfe 12 na daren yau sannan kowane kasuwanci za’a rufeshi.

 

Motocin dake kai mai gidajen mai da jami’an tsaro dana lafiya basa cikin wannan doka da kuma matafiya masu wucewa ta cikin garin Kaduna zuwa wasu garuruwa.

 

Gwamnatin tace domin wannan yanayi, ta tanadi abinci wanda aka siya da kudin ko ta kwana da ake ajiye dasu kuma za’a bi a rabawa masu karamin karfi a yayin wannan kulle.

 

 

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=hdlabarai.aplibwx

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *