fbpx
Tuesday, March 2
Shadow

Gwamnatin jihar kano ta bada ka’idojin sallar EId da Juma’a

Gwamnatin jihar kano ta bayyana sharudan sallar Eid da ta juma’a bisa la’akari da ka’idojin cutar Coronavirus kamar yadda kawararrun masana kiwan lafiya suka ambata kafin sallar Eid da Juma’a mai zuwa.

Hakan na kunshe ne a wata sanarwa da babban sakataran yada labarai na gwamna Abba Anwar ya fitar, wanda jaridar Daily trust ta rawaito.

Dangane da ka’idodin da aka sanya sun hada da gudanar da salla a cikin sa’a daya don bawa mutane damar warwatsewa cikin sauri.

Haka zalika wajibi ne ga duk wanda yake son shiga masallaci ya tabbata ya sanya abin rufe hanci. Don kare kansa da sauran mutane. Kuma Za’a sanya ruwa da sabulu a ƙofar masallaci sabuda ga duk wanda ke halartar sallar dole ne ya wanke hannunsa.

 

 

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *