fbpx
Monday, January 18
Shadow

Gwamnatin jihar Kano ta nemi hukumar NDLEA da ta gudanar da gwajin kwayoyi ga ‘yan takarar zaben kananan hukumomin jihar

Gwamnatin jihar Kano ta nemi hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA da ta gudanar da gwajin kwayoyi ga dukkan ‘yan takarar jam’iyyar  (APC) a zaben kananan hukumomin jihar da su ka hada da   shuwagabanin karamar hukumar da kansiloli.

Wannan na kunshe ne ta cikin wata wasika da ta fito daga Ofishin Sakataren Gwamnatin Jihar, Alhaji Usman Alhaji wanda ya samu sa hannun daga Sakatariya ta din-din kan sha’anin al’amuran siyasa Hajiya Bilkisu Shehu Mai Mota.

Sanarwar wacce Sakataren yada labarai Uba Abdullahi ya baiwa manema labarai ta ce gwajin ya kasance wani bangare ne na kokarin tabbatar da kyakkyawan aiki da taka tsantsan da bin diddigin dabi’un zababbun shuwagabannin da  za a baiwa jagorancin Jama’a.

 

 

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *