fbpx
Tuesday, August 9
Shadow

Gwamnatin jihar kano ta shirya sallamar al’majirai 2000 da aka kebe a ranar litinin

A ranar Lahadin da ta gabata ne Gwamnatin Jihar Kano ta ba da tabbacin cewa sama da Almajiris 2000 dake killace a cibiyoyin killa cewa dake kiru da karaye za a sallame su a ranar litinin 18 ga watan mayu.

Kwamishinan Ilimi na Jiha kuma Shugaban Kwamitin Kula da ‘Yan makaranta Almajiris Muhammadu Sanusi Kiru ne ya tabbatar da hakan ga Solacebase a ranar Lahadin da ta gabata yayin ziyarar cibiyoyin biyu a kananan hukumomin Kiru da Karaye inda sama da Almajiri 2000 suka keɓe.

Muhammadu Sanusi Kiru ya ce an dawo da mafi yawan Almajirin ne daga wasu jihohin kuma za a mika su ga iyayensu a kananan hukumomi daban-daban na jihar.

Karanta wannan  Hotuna: Kungiyar kiwon lafiya ta kaiwa shugaba Buhari ziyara a fadarsa

A cewar sa duk da haka wasu daga cikinsu wadanda ke nuna alamun rashin lafiya za a ware su kafin a mayar da su ga iyayensu,” in ji Alhaji Kiru.

Kwamishinan ya kuma yi watsi da zargin, na rashin kula da yaran ina ya bayyana cewa an wadatar da su da wadatattun kayan more rayuwa a cibiyoyin da aka kebe su.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.