fbpx
Tuesday, July 5
Shadow

Gwamnatin jihar Kano Ta Ware Naira Miliyan 245 Don Aurar da Mutanen Jihar Mabukata

Gwamnatin Jihar Kano a Nigeria ta zartas da ware kudade da suka kai Naira Miliyan 245 don tallafawa dimbin  mata da  maza da suka kai minzalin yin aure amman babu wuri, don su yi aure da tallafin aljihun Gwamnati.
Kwamishinan Watsa labarai na jihar Malam Mohammed Garba ya sanar da haka  a cikin wata sanarwa a Kano Asabar.
Kazalika ya fadi cewa an ware wasu kudaden Naira Miliyan 244 don baiwa kungiyar wasan kwallon kafa ta Kano Pillars.
Sanarwar na cewa Gwamnatin ta kuma ware kudade Naira Miliyan 29.3 don yiwa dabbobi alluran rigakafin cutuka wanda aka dakatar da yi shekaru uku da suka gabata.
Har ila yau yace an ware wasu kudaden da suka kai Naira biliyan 1.2 don gyara hanyar Ahmadu Bello Way, dake Kano sai kuma wasu Naira miliyan 212.9 don gyara rukunin dakunan mata na Dangote a Jami’ar Jihar Kano ta kimiya da Fasaha dake Wudil.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.