Saturday, April 4
Shadow

Gwamnatin jihar Katsina ta ba da sanarwar dakatar da sallar Juma’a da kuma ayyukan coci a duk fadin jihar

Gwamnatin jihar Katsina ta ba da sanarwar dakatar da sallar Juma’a da kuma ayyukan cocin a duk fadin jihar. Kwamishinan yada labarai na jihar, Abdulkarim Sirikam a cikin wata sanarwa da ya bayar ga manema labarai a ranar Alhamis ya ce sauran taron jama’a kamar bikin aure da siyasa suna duka a takaita su.

Ya ce ana gargadin jama’a da su takaita dukkan tarurrukan da zasuyi saboda gargadin da Cibiyar Kula da Cututtuka ta Najeriya (NCDC) ta yi game da saurin bazuwar cutar COVID-19 a kasar.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=hdlabarai.aplibwx

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *