fbpx
Monday, August 15
Shadow

Gwamnatin jihar Katsina ta sake dakatar da tuka babura kan matsalar tsaro

Hukumar ‘yan sanda ta jihar Katsina ta tace gwamnati ta sake sa doka kan masu tuka babura a jihar, cewa daga karfe shida na safe zuwa goma na dare kadai zasu rika aiki.

Gwamnatin ta sake saka wannan dokar watanni hudu bayan ta dakatar da dokar gabanin azumin watan Ramadana daya gabata.

Inda ta bayyana cewa ta dawo da wannan dokar ne  saboda matsalar tsaron da jihar ke fama dashi.

Mai magana da yawun hukumar ne ya bayyana hakan ranar litinin, woto SP Gambo Isa.

Leave a Reply

Your email address will not be published.