fbpx
Wednesday, June 29
Shadow

Gwamnatin Jihar Kebbi Ta Daure Ni A Gidan Yari Na Kwana Biyu, Kuma Tana Sake Kokarin Daure Ni, Akan Laifin Na Yi Kira Da Ta Gyara Harkar Ilmi, A Karamar Hukumar Mu Ta Arewa Dake Jihar Kebbi, A Cewar Matashi Comr Mustapha Ibrahim Zango

Gwamnatin Jihar Kebbi Ta Daure Ni A Gidan Yari Na Kwana Biyu, Kuma Tana Sake Kokarin Daure Ni, Akan Laifin Na Yi Kira Da Ta Gyara Harkar Ilmi, A Karamar Hukumar Mu Ta Arewa Dake Jihar Kebbi, A Cewar Matashi Comr Mustapha Ibrahim Zango

Duba da ganin irin matsalar yankin mu na karamar hukumar Arewa take ciki na fannin ilimi yasa na ma yarda hankali kan hanyoyin da za’abi wajen ganin an inganta harkar ilimi a karamar hukuma ta, amma duka bansamu nasara ba.

Shine nayi rubutu kan timeline dina na Facebook kamar haka:

“Ina Kira zuwa ga gwamnatin jahar Kebbi da ta mayadda hankali kan fannin ilimi, musamman a Arewa Local government domin ansamu tabar barewar ilimi a yanzu ba kamar waccan gwamnati da akayi a baya ba”.

Dalilin wannan rubutun yasa aka turani gidan yari tsawon kwana biyu. Kuma alkali ya bayyana zai yankemin hukuncin zama gidan yari na shekara biyu ko kuma Bulala a tsakiyar kasuwa, a ranar alhamis mai zuwa, 19 May 2022.

Karanta wannan  Gwamnan jihar Ondo ya goyi bayab Matawallen Zamfara na cewa 'yan jihar su mallaki bindugu don kare kawunansu

Shugaban kula da hukumar ilimi na Arewa Local government Sani Ahmad Umar, ne ya jagoranci karar a matakin Police Station da kuma kotu.

A yanzu Ina kan beli zuwa ranar Alhamis zamu koma kotu.

Nine nayi takarar kansila a karkashin jam’iyyar PDP a Kangiwa Ward a zaben da ya gabata.

Nine shugaban kungiyar Kangiwa Youth Dev. Association. Nine wanda ya jagoranci kawo sassaucin harkar tsadar Aure a garin Kangiwa.

Kuma nine na jagoranci shawo kan matsalar wutar lantarki a garin Kangiwa da kauyuka.

Da wannan nike kira ga Gwamnan jihar Kebbi da ya shiga wannan lamarin domin a mini adalci a cikin wannan lamarin.

~ Wannan shine korafin matashi Comr Mustapha Ibrahim Zango.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.