Mataimakin Gwamnan Jihar Kebbi, Samaila Yombe Dabai mai (ritaya), ya sha alwashin cewa gwamnatin jihar zata zakulo masu aikata laifuka a cikin kungiyar ‘Yan-Sakai wadanda ke fakewa suna aikata laifuka daban-daban a yankin Masarautar zuru.
Dabai ya shaida hakan ne a yayin rangadin da ya gudanar a yankunan masarautar, A yayin da yake zantawa da manema labarai a Birnin Kebbi, Mataimakin gwamnan ya bayyana cewa wasu bata gari suna fakewa da aikin ‘yan sintiri suna aikata laifuka.
A cewarsa Gwamnati ta gano hakan kuma tana shirin Daukan mataki domin dakile masu aikata miyagun laifuka a jihar.