fbpx
Wednesday, March 3
Shadow

Gwamnatin Jihar Kebbi za ta dauki nauyi dalibai 300 zuwa kasashen wajen domin yin karatun likitanci, fasaha da kuma kere-kere

Gwamnatin Jihar Kebbi ta ce za ta dauki nauyin dalibai sama da 300 zuwa kasashen Indiya da Turkiya da kuma Cyprus don karatun Likitanci, Kimiyyar Kiwan lafiya, fasaha da Injiniya.

Kwamishinan Ilimi mai zurfi, Mukhtar Bunza ne ya sanar da hakan yayin rantsar da sabbin shuwagabannin kungiyar Kwadago ta kasa reshen jihar Kebbi, NUKESS, wanda aka gudanar a Kwalejin Kimiyyar Jinya da ke Birnin Kebbi, ranar Lahadi.

Bunza, wanda ya samu wakilcin babban sakatare a ma’aikatar, Halima Dikko, ya ce saboda lura da mahimmancin ilimi ga ci gaban al’umma, Gwamna Bagudu ya jagoranci gwamnatin a tsawon shekaru tare da ba da fifiko kan bangaren ilimi wanda hakan yasa aka samu nasarorin da dama.

Ya kara da cewa wannan Gwamnatin ta Sanata Abubakar Atiku Bagudu ta shirya tsaf don daukar nauyin dalibai sama da 300 zuwa kasashen Indiya, Turkiya da Cyprus don karatun Likitanci, Kimiyyar Kiwon Lafiya, da harka Injiniyanci.

A cewarsa, wannan ya tabbatar da manufar gwamnan na tabbatar da cewa an samar da ingantaccen ilimi ga ɗalibai don ba su damar yin takara da takwarorinsu a duniya.

Kwamishinan ya tabbatar da cewa duk cibiyoyin ilmantarwa a cikin jihar sun sami kulawa ta musamman don samun manyan matsayi da cigaba mai amfani.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *