Shanaye 20 sun mutu a jihar Kogi jiya ranar alhamis, wanda ake kyautata zaton cewa an masu guba ne.
Biyo bayan hakan gwamnatin jihar ta bukaci mazauna jihar cewa kar suci jan nama na tsawon sati guda musamman wa’yanda ke cikin garin Lokoja.
Gwamnatin ta sanar da hakan ne ta bakin darektan likitocin dabbobi Muhammad Salau Tarawa, wanda yace sun hada kai da jami’ai domin gano makiyayan da suka aikata bannar kuma a hukunta su.